23 Yuni 2026 - 10:37
Source: ABNA24
Ana Ci Gaba Da Zaman Juyayin Ashura A Makarantar Ma’ahadur Rasul Al-Akram (SAWW) + Hotuna

An ci gaba da gudanar da zaman Juyayin Ashura a Makarantar Ma’ahadur Rasul Al-Akram (SAWW) Kudan a rana ta shida, inda shugaban makarantar, Sheikh Isma’il Yusha’u Kudan, ya jagoranci zaman cikin wani yanayi mai cike da nutsuwa, tausayi da sanya zukata cikin zurfin tunani.

A cikin jawabin nasa, Sheikh ya yi bayani mai faɗi game da abubuwan da suka shafi Waki’ar Karbala, inda ya mayar da hankali a bayaninshi kan yadda Ashura ba wai kawai tarihi ba ne na wani alhini da ya shuɗe, sai dai makaranta ce ta rayar da zukata, gyaran rayuwa, da kuma sanya mutum ya sake duba matsayinsa domin kasancewa cikin masu tafiya a kan tafarkin Imam Husain (AS), tafarkin gaskiya, sadaukarwa da tsayuwa akan gaskiya.

A ƙarshen zaman, Sheikh ya karanto irin mawuyacin halin da Imam Husain (AS), iyalansa da sahabbansa suka tsinci kansu a ranar Ashura; ƙishirwa, ƙunci, Wanda yake kewaye da zalunci. Cikin salo mai ratsa zuciya ya zayyana waɗannan abubuwa har kalamansa suka shiga zukatan mahalarta, suka girgiza zukata tare da sanya idanu zubar da hawaye cikin juyayi da alhini ga musibar Karbala.

“Aminci ya tabbata gareka ya Imam Husain, da Aliyu ɗan Husain, da ‘ya’yan Husain, da sahabban Husain A.S)”.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha